Mun gamsu da kamun ludayin Gwamna Zulum – Jam’iyyar PDP

Mun gamsu da kamun ludayin Gwamna Zulum – Jam’iyyar PDP

Babbar jam’iyyar PDP ta bayyana gamsuwarta da kamun ludayin gwamnan jahar Borno na jam’iyyar APC, Farfesa Babagana Umara Zulum sakamakon yadda yake tafiyar da harkar tsaro a jahar, tare da sauran ayyuka.

Shugaban sashin jam’iyyar PDP, Usman Badeiri ne ya bayyana haka ne inda yace Gwamna Zulum ya basu mamaki duba da manyan ayyukan da yake gudanarwa a jahar Borno, duk kuwa da cewa dan jam’iyyar APC ne.

KU KARANTA: Yan siyasan Najeriya za su samu karin albashi – Hukumar rarraba kudaden gwamnati

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban jam’iyyar, Usman Badeiri ya jaddada cigaba da zama a cikin jam’iyyar PDP daram dam dam, ba ma shi kadai ba, hatta shuwagabannin jam’iyyar a matakin jaha, kananan hukumomi da mazabu ba zasu fita daga cikinta, inji shi.

Jam’iyyar PDP ta shiga mawuyacin hali a jahar Borno tun gabanin zaben 2015, wanda ya raba jam’iyyar gida biyu, bangaren Alhaji Usman Badeiri wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP tun farkonta, da bangaren Alhaji Zanna Gaddama, wanda ya shiga PDP daga APC gab da zaben 2015.

Badeiri yace shi da shuwagabannin jam’iyyar a matakin jaha, kananan hukumomi da mazabu sun dauki matakin kawar da bambamce bambamcen siyasa domin su karrama gwamnan jahar Borno sakamakon kyawawan ayyukan da yake gudanarwa.

“Sai da muka dauki watanni 8 kafin mu gamsu da cewa lallai gwamnan jahar Borno yana aiki, kuma ya kamata mu yaba masa domin jahar Borno ta yi sa’ar samun gwamna irin Zulum duba da kokarin da yake yi wajen yaki da Boko Haram.Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel