Tsohon shugaban kasa IBB na nan da ransa, Inji hadimansa

Tsohon shugaban kasa IBB na nan da ransa, Inji hadimansa

Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB na nan da ransa, kuma cikin koshin lafiya kamar yadda wasu manyan hadimansa, kuma na hannun damansa suka tabbatar.

Jaridar The Nation ta ruwaito hadiman nasa sun bayyana haka ne biyo bayan jita jitan da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani na cewa wai IBB ya rasu da sanyin safiyar litinin, 27 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Zazzabin cutar lassa: Likitoci 7 da ma’aikatan jinya 5 na cikin tsaka mai wuya a jahar Adamawa

Amma majiyar ta tabbatar da cewa Babangida na cikin koshin lafiya, kuma zuwa lokacin da ta samu rahoto ma an bayyana mata yana gidansa yana cin abinci, bugu da kari yana cikin annushuwa da walwala.

Daga cikin hadiman Babangida akwai wanda yace: “A yanzu da nake magana ina gidan Baba, yana sanye da malum malum babbar riga, kuma yana cin abinci ne.”

Shi ma wani hadimin nasa yace: “Mutuwa baa bin boyewa bane, idan Babangida ya mutu a yau, ba zai taba zama jita jita ba, ba’a iya boye mutuwa saboda abu ne wanda ke kan kowa, kuma idan ya faru dole kowa ya sani.”

Sai dai ba wannan bane karo na farko da ake danganta ma IBB mutuwa a kafafen sadarwar zamani, sakamakon an dade ana jita jitan ya mutu, sai kuma daga baya a gano ba gaskiya bane.

Ko a makon data gabata an hangi mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusu II ya kai ma IBB ziyara a gidansa dake kan dutse, a garin Minnan jahar Neja.

Amma akwai rahotannin da suka nuna cewa IBB ba shi da cikakken lafiya saboda matsalar kafa da yake fama da ita, domin kuwa a kan kujera na musamman yake zama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel