Da dumi-dumi: Gwamnan Bauchi ya sallami shugaban ma’aikatan gidan gwamnati

Da dumi-dumi: Gwamnan Bauchi ya sallami shugaban ma’aikatan gidan gwamnati

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya amince da murabus din Shugaban ma’aikatansa, Alhaji Abubakar Kari.

A cewar wani jawabi dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Sabiu Baba, ya ce gwamnan ya kuma amince da nadin Ladan Salihu a matsayin sabon Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, ba tare da bata lokaci ba.

Kafin nadin nasa, Salihu ya kasance kwamishinan labarai da sadarwa a jihar.

Gwamnan ya yiwa Kari godiya akan aikin da ya yi a lokacin da yake kan kujerar Shugaban ma’aikatansa sannan ya yi masa fatan alkhairi a gaba.

A cewar sanarwar; “Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya amince da ajiye aiki bisa radin kashin kai na Alhaji Abubakar Kari, a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar.

KU KARANTA KUMA: An rantsar da Gwamna Yahaya Bello a karo na biyu

“Gwamnan ya kuma gode masa a bisa bayar da gagarumar gudunmawa a lokacin da yake rike da mukamin shugaban ma’aikatan, sai yayi masa fatan samun rayuwa mai kyau a gaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel