Arewa za ta yi tasiri wajen zaben sabon Shugaban kasa – Shugaban NEF

Arewa za ta yi tasiri wajen zaben sabon Shugaban kasa – Shugaban NEF

Nasarar duk wani ‘Dan takarar da zai yi nasara a zaben 2023 ya danganta ne da goyon-bayan da ya samu daga Yankin Arewacin Najeriya.

Farfesa Yimi Sen, wanda shi ne Darekta Janar na kungiyar NEF ta Dattawan Arewa ya bayyana wannan a wata hira da ya yi da ‘Yan jarida.

Yimi Sen ya bayyana cewa har yanzu kungiyarsa ta Dattawan Yankin Arewa ba su tsaida matsaya kan wanda za su marawa baya ba.

Darektan na NEF ya nuna cewa ba ya adawa ga duk wanda zai gaji shugaba Buhari muddin ya cancanci rike kasar, ko daga ina ya fito kuwa.

Farfesan ya yi wannan jawabi ne a doguwar hirarsa da Jaridar Vanguard kwanan nan wanda aka fitar a Ranar 26 ga Watan Junairun 2020.

“A nawa lissafin, 2023 ta mai rabo ce. Yanzu akwai mutanen da za su fara ikirarin ya kamata mulki ya dawo hannunsu a tsarin kama-kama.”

KU KARANTA: PDP ta nada sabon Shugaban Gwamnonin Jihohin Najeriya

Arewa za ta yi tasiri wajen zaben sabon Shugaban kasa – Shugaban NEF
Ana tunanin Asiwaju Bola Tinubu zai nemi ya gaji Buhari
Asali: Facebook

”Na san akwai kira da ake yi da babbar murya cewa ya kamata mulki ya koma Kudu maso Gabas."

“Amma matsalar wannan ita ce za mu yi fama da ko za su saurari Nnamdi Kanu ne, ko kuma za su saurari ‘Yan siyasar da ke yankin.” Inji sa.

Da aka tambayesa ko NEF za ta goyi bayan Bola Tinubu a matsayin Magajin Buhari, sai ya ce su na son ganin shugaban da zai yi jagoranci da kyau.

“Na damu ne da yadda Najeriya ta gaza cigaba yadda ya dace daga samun ‘yancin kai zuwa yau.”

Farfesan ya cigaba da cewa: "A matsayina na Mai bincike da hasashe, na yi rubuce-rubuce a kan wannan. Har na gaji, ba na son magana a kai”

“Ina son ganin an samu sauyin yanayi, kuma na yi amanna cewa shugabannin da su ka rike Najeriya bayan samun ‘yanci sun gaza kai mu ga ci.”

Farfesan ya yadda cewa daga lokacin mulkin Soji zuwa yanzu, mulki ya dade sosai a Arewa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel