Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kama ma'ajin fadar sarki Sanusi

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kama ma'ajin fadar sarki Sanusi

A wani labari da Legit.ng taci karo da shi a shafin Salihu Tanko Yakasai, daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Kano, hukumar yaki da cin hanci da rasha wa ta Kano ta kama ma'ajin fadar Kano bisa zargin tafka badakala.

A takaitaccen sakon da Yakasai ya wallafa a shafinsa na Tuwita (@dawisu) ya bayyana cewa, "hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kama ma'ajin fadar sarkin Kano a kan sayar da wani fili da fadar Kano tayi ba bisa ka'ida ba,".

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano a karkashin shugabancin Muhyi Magaji Rimin Gado ta dade tana binciken fadar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a kan zargin tafka badakala da almubazzaranci da kudaden fadar.

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kama ma'ajin fadar sarki Sanusi
Sarki Sanusi II
Asali: Twitter

Sai dai, wasu da dama na ganin cewa binciken da hukumar ke yi wa fadar ba zai rasa nasaba da tsamin da dangantaka ta yi a tsakanin fadar da gwamnatin jihar ba.

DUBA WANNAN: Wani mutum ya yi fim din batsa a arewacin Najeriya da 'yammata da matan aure

Yakasai bai bayyana a kan wanne fili ne hukumar yai da cin hancin ta kama Ma'ajin ba. Kazalika, bai bayar da cikakken bayani a kan lamarin ba.

Legit.ng zata kawo karin bayani da zarar ta samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel