Yan Boko Haram sun sha kashi a hannun sojoji, sun gudu sun bar motarsu (bidiyo)

Yan Boko Haram sun sha kashi a hannun sojoji, sun gudu sun bar motarsu (bidiyo)

Dakarun sashi na 7 na rundunar sojin Najeriya sun sha karfin wasu mayakan Boko Haram a hanyar Maiduguri-Damaturu da ke jihar Borno a yammacin ranar Lahadi.

Yan ta’addan sun kaddamar da hare-hare daban-daban a kan hanyar cikin wata guda da ya gabata.

A wani faifan bidiyo da jaridar TheCable ta wallafa an gano sojoji na bude wuta ta bangaren abokon hamayyarsu.

An jiyo wani soja yana ihun “Bude wuta, Bude wuta! Kashe su, a gama dasu yayinda karan harbi ke tashi a sama.

“Kalli wata motar bindiga a chan... Boko Haram sun yasar da motar bindigar,” cewar wani soja yayinda aka cigaba da harbin.

Kusa da karshen bidiyon mai tsawon minti biyu da sakan 58, wani soja ya ce: “Kamar yadda kuke gani, mun yi nasara kan Boko Haram a yau. Sun yasar da motarsu.

Sannan daga bisani sai wasu sojoji suka dunga dudduba motar da yan ta’addan suka bari kafin daga bisani suka dauke shi daga wajen.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CAN ta yi martani ga labarin haihuwar Leah a hannun yan ta’adda

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labarin kuma, mun ji cewa Mutane uku sun mutu yayin da wasu 13 suka samu munanan rauni yayin da wasu mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai harin kunar bakin wake a wani masallaci dake karamar hukumar Gwoza na jahar Borno.

Daily Trust ta ruwaito wani sojan sa kai na Civilian JTF ne ya bayyana haka, inda yace lamarin ya faru ne yayin da Musulmai suke sallar Asubahi da safiyar Asabar, 25 ga watan Janairu a kauyen Bulabulin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng