An kai harin makami mai linzami ofishin jakadanci Amurka dake Baghdad
Wani labari da dumi - duminsa da Legit.ng ta samu daga shafin 'Spectator Index' dake shafin Tuwita ya bayyana cewa an sake kai harin makamin roka mai linzami a kan ofishin jakadancin kasar Amurka dake Baghdad, babban birnin kasar Iraqi.
A cikin takaitaccen sakon da 'Spectator Index' ta wallafa, an bayyana cewa harin ya lalata wani bangare na ofishin jakadanci da ake cin abinci.
"Da duminsa: An kai harin makamin roka mai linzami a ofishin jakadancin kasar Amurka dake Baghdad a yau, an lalata bangaren cin abinci," a cewar 'Spectator Index'.
Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko kasa data dauki alhakin kai harin, kazalika, babu rahoton asarar rai.
Ko a ranar 12 ga watan Janairu saida aka kai wasu munanan harin rokoki sansanin sojin Balad da sojojin kasar Amurka ke zaune a birnin Baghdad na kasar Iraqi, kamar yadda jami'an tsaro suka tabbatar.
A wancan lokacin, AFP ta ruwaito cewa sojojin Amurka sun arce daga sansanin yayin da sojojin kasar Iraqi hudu suka jikkata a harin.
Wani jami'in dan sanda a yankin, Salah-Al-Din, ya bayana cewa rokokin sun dira cikin sansanin sojojin saman.
A farkon watan Janairu ne kasar Iran ta harba rokoki masu linzami guda zuwa 20 sansanin sojojin Amurka dake Iraqi domin mayar da martani a kan kisan babban hafsan rundunar sojojin Iran, Qassem Soleimani, da Amurka ta yi.
DUBA WANNAN: An yi fim din batsa da 'yammata da matan aure a arewacin Najeriya
An harba rokokin ne zuwa sansanin Ayn Al Asad da Sansanin Erbil Asad da misalin karfe 5:30 na yamma, kuma da alamun a kalla sojojin Amurka 80 sun hallaka, a cewar wasu rahotanni.
Amma Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu dan Amurkan ko daya da ya samu rauni a harin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi.
Trump ya yi kira ga kasashen Turai, Rasha, Sin, Jamus da Ingila a kan su fita daga yarjejeniyar nukiliya da suka shiga a shekarar 2015.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng