Saudi Arabia za ta saye Kungiyar Newcastle United a kan £350m

Saudi Arabia za ta saye Kungiyar Newcastle United a kan £350m

Mun samu labari cewa Kasar Saudi Arabia ta na tattaunawa da kungiyar Newcastle United domin sayen kulob din daga hannun Mai rike da ita.

Gidan yada labarai na Reuters ta kawo rahoto cewa kasar Larabawan ta na son sayen Newcastle a kan kudi fam miliyan £340 idan har an tsaida ciniki.

Kasar za ta biya wannan kudi ne daga babban asusun gwamnati na Sovereign Wealth Fund kamar yadda wata jaridar Wall Street ta bayyana.

Fitaccen Attajirin nan, Mike Ashley, shi ne wanda ya ke da mallakar kungiyar kwallon kafar. Tun shekarar 2007, Mutumin Birtaniyan ya saye kulob din.

Hukumar asusun kasar Saudi tare da Amanda Staveley ne su ke jagorantar tattaunawar sayen kungiyar, kuma an ce maganar ta na kasa ta na dabo.

KU KARANTA: Kungiyar Inter Milan ta karbi aron 'Dan wasan Najeriya

Saudi Arabia za ta saye Kungiyar Newcastle United a kan £350m
Saudi ta na son sayen Newcastle daga hannun Mike Ashley
Asali: Getty Images

An dade da sa kungiyar a kasuwa domin a saida ta. A ‘yan shekarun baya, har an taya kungiyar a kan kudi fam miliyan £250 amma ba a sallama ba.

Rahotannin sun bayyana cewa ani Mai magana da yawun bakin kungiyar, ya yi gum da aka yi masa tambaya game da wannan batu a Ranar Lahadi.

Mista Mike Ashley bai da farin jini a wajen Magoya bayan kungiyar kwallon. Wannan ya sa ake ta faman yi masa zanga-zanga har ta kai ga yin bore.

Mafi yawan kungiyoyin kwallon Ingila su na hannun Baki ne. Yanzu haka Amurkawa ne ke da Arsenal, Liverpool da kungiyar Manchester United.

Man City ta na hannun wasu Larabawan kasar UAE ne. A bara idan kun tuna, an yi ta rade-radin cewa Khaled bin Zayed Al Nehayan zai saye Newcastle.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel