Zaben maye gurbi: Dattijan APC a Kano sun juya wa Kofa baya, dan takarar PDP na kan hanyar lashe zabe

Zaben maye gurbi: Dattijan APC a Kano sun juya wa Kofa baya, dan takarar PDP na kan hanyar lashe zabe

Dattijan Jam'iyyar APC a jihar Kano sun juya wa Abdulmumin Jibrin Kofa, tsohon dan majalisar wakilai daga mazabar Kiru da Bebeji, baya, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

A ranar Asabar hukumar zabe mai kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zabuka a kan wasu kujerun majalisar dokokin jihar Kano guda hudu da kuma na majalisar tarayya guda uku da suka hada da Kiru/Bebeji, Tudun Wada/Doguwa da Kumbotso.

Baraka ta kunno kai a tsakanin tsohon dan majalisa Kofa da dattijan jam'iyyar APC a jihar Kano bayan ya wallafa wani rubutu dake nuna rashin goyon bayansa a kan yadda zaben raba gardama ya gudana a tsakanin Ganduje da Abba Gida - Gida.

A takaitaccen sakon da ya wllafa a shafinsa na Tuwita ranar 11 ga watan Maris, Kofa ya rubuta, "abubuwan da suka faru a Kano a 'yan sa'o'in da suka wuce abun kunya ne da Alla - wadai. Dole ne a matsayinmu a shugabanni mu kasance masu sanin ya kamata da yin abin da ya dace da kuma yin biyayya ga zabin jama'a. A kowanne zabe akwai zakara. Kawai a bawa wanda ya samu nasara kambunsa."

A ranar 11 ga watan Agusta ne shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Bebeji, Sulaiman Sabo Gwarmai, ya sanar da cewa sun dakatar da Abdulmumin Kofa bisa zarginsa da cin dunduniyar jam'iyya.

Zaben maye gurbi: Dattijan APC a Kano sun juya wa Kofa baya, dan takarar PDP na kan hanyar lashe zabe
Abdulmumin Kofa
Asali: Twitter

Dattijai da jagororin jam'iyyar APC a jihar Kano sun hango damar daukan fansa a kan Abdulmumin Kofa bayan wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta soke zabensa tare da bayar da umarnin sake gudanar da sabon zabe.

DUBA WANNAN: Fim din batsa da 'yammatan arewa ya bayyana a yanar gizo, daya daga cikin matan bidiyon ta kashe kanta

Jaridar Daily Nigerina ta rawaito cewa dattijan APC a jihar Kano sun kulla yarjejeniya da dan takarar jam'iyyar PDP, Ali Datti Yako, tsohon shugaban karamar Kiru, a kan zasu goya masa baya bisa sharadin cewa zai koma jam'iyyar APC bayan an kammala zabe.

A cewar Daily Nigerian, sakamakon zaben dake fitowa daga mazabu da kananan hukumomin da ake gudanar da zabukan, suna nuni da cewa jam'iyyar APC ce a kan gaba amma banda a mazabar Kiru da Bebeji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel