Ba a wannan lokacin ya kamata shugaba Buhari yayi mulki ba - Kashim Shettima

Ba a wannan lokacin ya kamata shugaba Buhari yayi mulki ba - Kashim Shettima

- Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya ce kamata ya yi sai nan da shekaru 50 shugaba Buhari ya kamata ya mulki kasar nan

- Tsohon gwamnan kuma sanata a yanzu ya ce akwai bukatar a jinjinawa shugaba Buhari a kan yadda tattalin arzikin kasar nan ke habaka

- Sanatan ya yi tsokaci a kan dimbin dukiyar da wasu tsoffin gwamnoni ke karba a matsayin kudin fansho

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya ce kamata yayi sai nan da shekaru 50 ne Shugaba Muhammadu Buhari zai mulki Najeriya, domin ta haka ne za a fi ganin tasirin mulkinshi.

Shettima ne ke wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa "burin da 'yan Najeriya suka dora kan mulkin shugaban ya yi yawa".

"Wani lokacin sai na ji kamar cewa nan da shekaru hamsin ne ya kamata Buhari ya mulki kasar nan saboda irin abubuwan da wasu ke gani a matsayin gazawarsa su ne ainahin nasarori da kwarewar shi," cewar Sanatan.

Ya kara da cewa "Buhari yana nada mutum a kan mukami, ya kuma sakar mishi mara ya yi duk abin da ya ga ya dace tare da bin ka'ida da sanin ya kamata. Hakan kuwa ba zai yuwu ba a tsarin Najeriya."

Sanata Shettima ya yi kira ga 'yan Najeriya da su jinjinawa Buhari kan yadda yake farfado da tattalin arzikin kasar nan.

"Wannan na daya daga cikin bangarorin da wasu ba sa so su jinjinawa shugaban duk da nasarorin da ya samu saboda tattalin arziki ya tabarbare matuka a lokacin da ya zo.

"Alal hakika ya farfado da tattalin arziki. A karon farko ga shi muna fadada kasafin kudinmu, ana tunkarar manyan ayyuka na ci gaban kasa."

Ya kara da cewa "ina ganin ba mu jinjina mishi kamar yadda ya cancanta."

Tsohon gwamnan jihar Borno din ya yi magana a kan dimbin kudaden da wasu tsaffin gwamnoni ke karba a matsayin fansho, da dalilin da yasa ya goyi bayan farfesa Babagana Zulum a matsayin magajin shi da batun 'yan matan Chibok.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel