Yanzu-yanzu: APC ta fasa shiga zaben maye gurbi a Akwa Ibom, ta bayar da dalili
- APC ta janye daga zaben raba gardama na Akwa Ibom
- Jamiyyar ta ce bata gamsu cewa INEC za ta gudanar da zabe na gaskiya da adalci ba
- Kazalika, wasu yan Najeriya sunyi kira ga INEC ta manta da batun zaben don kawai barnar kudu za tayi
Sakamakon abinda ta kira rashin gamsuwa da tsare tsaren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, jamiyyar All Progressives Congress (APC) a Akwa ta ce ta janye daga zaben raba gardama da aka shirya yi a ranar Asabar a Akwa Ibom.
Shugaban jamiyya na jihar, Ini Okopido ne ya sanar da hakan yayin taron manema kabarai da ya kira a ranar Juma'a.
Okopido ya ce laifin INEC ne shiyasa jam'iyyar ta janye daga zaben.
Bayan sanarwarsa wasu yan Najeriya a dandalin sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin.
DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu sun cimma matsaya kan Amotekun
Benedict Cool: "Sun barnatar da miliyoyin naira a kotu, yanzu kuma ba su son ayi zaben da suka yi ikirarin cewa su ne suka yi nasara a baya."
Usman Kayanta Aduku: "Menene amfanin yin zaben raba gardama idan idan har babban jamiyyar hamayya ta janye daga zaben"
Udoma Emmanuel: "Ya kamata a hukunta su. Kada INEC ta wahal da kanta wurin yin zaben domin barnar kudi da kayan aiki kawai za tayi."
Uchehi Reuben Ojindu: "Ba a sakin reshe a kama ganye, Akpabio mutum ne mai hikima."
Ogumba Ikenna: "Akpabio yana jiran su a kotun koli ko da bai shiga zaben ba. Ku tafi ku tambayi Hope Uzodinmma yadda ya yi nashi. Haka Najeriya ta ke."
Ejigbo Okai: "Akabio ba zai taba sake lashe zabe ko da ta kansila bane a rayuwarsa. Gwamnan su ya gama da shi."
Johnson Chinonso Ofoegbu: "Akwai alamun APC ta janye daga zaben ne domin ta tafi kotun koli domin tayi wani siddabaru."
Akamo Damilare Dreycool: "Mene yasa suka tafi kotu tun farko. Kawai suna wasa da hankulan mutane."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng