An damke wani namiji da ya yi shigan mata don a dauke shi aikin kula da gida

An damke wani namiji da ya yi shigan mata don a dauke shi aikin kula da gida

- Wata kotu mai daraja ta farko da ke yankin Karu a birnin tarayya ta yankewa wani matashi hukuncin shekaru 2 a gidan gyaran hali

- Mai shari'a Abdullahi Jibrin ya kama Chidera Sunday ne da laifin yin basaja a matsayin mace don ya samu aikin cikin gida na mata

- Kamar yadda ya ce, laifin abin hukuntawa ne a karkashin sashi na 79 da na 179 na dokokin Penal Code

Wata kotu mai daraja ta farko da ke yankin Karu a Abuja ta yankewa wani matashi mai suna Chidera Sunday hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali. Sunday mai shekaru 18 ya yi basaja ne inda ya bayyana a matsayin mace don ya samu aikin cikin gida.

A yau Juma'a ne Mai shari'a Abdullahi Jibrin ya yankewa Sunday mai shekaru 18 hukuncin zaman gidan gyaran halin na shekaru biyu ba tare da zabin tara ba, bayan ya amsa laifin shi a gaban kotun, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Da farko dai dan sanda mai gabatar da kara, Ayotunde Adeyanji, ya sanar da kotun cewa wani mutum mai suna Leonard Ezirike da ke Jikwoyi ya kawo koken ga ofishin 'yan sandan yankin Jikwoyi a ranar 22 ga watan Disamba.

DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa tsohon kwamishina hukuncin shekaru 19 a gidan gyaran hali

Adeyanju ya zarga cewa an kai masa Sunday ne a ranar 18 ga watan Disamba don ya fara aiki a matsayin 'yar aiki mace a gidansa.

"Bai sani ba Sunday ya hada kai da wata mai suna Happiness da wani Chinedu ne don ya bayyana a matsayin mace. Amma kuma a ranar 21 ga watan Disamba, sirikinsa ya kira shi inda ya sanar da shi cewa mai aikin nan ba mace bace, namiji ne," cewar Adeyanju.

Kamar yadda ya ce, laifin abin hukuntawa ne a karkashin sashi na 79 da na 179 na dokokin Penal Code.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel