Wani bawan Allah ya tsinci naira miliyan 9.7 a ATM sai ya mayar dashi cikin banki
George Condash ya tsinci kanshi a cikin wani yanayi mai cike da rudin duniya lokacin da ya ga wani akwati da ke dauke da kudi $27,000 (N9,760,500) a kusa da na’urar ATM a Michigan Credit Union a ranar Talata, 22 ga watan Janairu.
Sai ya yi wani abun bazata, inda ya dauki akwatin kudin sannan ya tuka motarsa zuwa Westland Federal Credit Union inda ya mayar da kudin, abun da ba kowa ne zai iya hakan ba, CNN ta ruwaito.
A wata hira a CNN, George ya ce a lokacin da ya daura kudin a wajen karban kudi na bankin, ma’aikatan bankin sun cika da mamaki.

Asali: UGC
Bidiyon tsaro da ke ATM din ya nuna wani mai gadi a lokacin da yake fitar da jakunkunan kudi daga motar silke. Mintuna 20 bayan nan ne aka gano George yana duba akwatin da aka bari a wajen.
Koda dai akwatin na dauke da rubutun $40,000 (N14,460,000), $27,000 (N9,760,500) kawai aka bari ciki bayan lodi. Bankin ta kuma bayyana cewa ta ba bawan Allan tukwicin wasu kudade da bata bayyana ba.
KU KARANTA KUMA: Shugabar matan Kannywood ta kare jarumai mata da ke yawon bude ido a kasashen waje
Manajar bankin, Alicia Stewart, ta bayyana cewa da ace George bai dawo da kudin ba, bankin za ta gano shi ta kamarar ATM din sannan ta kamo shi ta lambar motarsa.
Da yake magana a kan mayar da kudin, George ya ce kudin ba nashi bane kuma duk wani mutum mai amana zai yi abun da ya yi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng