Gwamnatin Buhari ta kashe naira Tiriliyan 1.7 kan wutan lantarki da yake a durkushe – El-Rufai

Gwamnatin Buhari ta kashe naira Tiriliyan 1.7 kan wutan lantarki da yake a durkushe – El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya koka kan yadda gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kasha makudan kudi har naira Tiriliyan 1.7 a harkar wutan lantarkin kasar alhalin gashi har yanzu kasar na fama da duhu.

El-Rufai ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci gaba da kashe wadannan kudae masu yawan gaske alhalin ba a ganin wata fa’ida tattare da lamarin.

Har ila yau gwamnan wanda ya yi wannan bayani a taron Kwamitin Inganta Tattalin Arzikin Kasa, ya roki mutane da su kara hakuri zuwa lokacin da kwamitin sa zata kammala bincike akan wannan sashe kafin su ce wani abu.

Ya ce: “Gaba daya maganar wutan lantarki ya tabarbare a kasar nan. Kama daga yadda ake biyan kudin wutan da ake sha zuwa yadda tun farko aka yi cinikin saida kamfanonin samar da wutan lantarkin duk matsala ne a kasar.

“Idan ba haka ba ta yaya za a ce wai an saida kamfanin ga ‘yan kasuwa sannan kuma gwamnati ta narka kudi har naira Tiriliyan 1.7 cikin shekaru uku bayan kuma an saida kamfanin. Wannan babban abin tambaya ne.

“Ina rokon mutane da a dan dakata tukunna sai mun mika wa gwamnati rahoton binciken mu kafin idan akwai abin cewa sai a fito a yi magana.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso na shirin dawowa APC don takarar shugaban kasa a 2023 – Ganduje

“Kuma lallai shawarwarin da za mu bada ba zai yi wa wasu dadi ba, amma dai dole mu dauki wannan mataki idan muna so wuri irin haka ya gyaru sannan ya amfani mutanen Najeriya.

“Haka kuma idan za a fadi gaskiya, akwai akalla mutane miliyan 80 a kasar nan da basu samun wutan lantar ki kwata-kwata. Hakan ba za a bari ya ci gaba sannan kuma ace wai bayan an saida kamfanin wutan, gwamnati ta kashe naira Tiriliyan 1.7. Akwai abin lallai ayi zurfin tunani akai.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel