Rikici ya barke yayin da miji ya fadawa matarsa cewa zai je Borno kasuwanci, ashe kishiya ya tafi ya karo mata
- Wata fusatacciyar matar aure ta yi bayanin yadda mijinta ya ci amanarta babu zato balle tsammani
- Mijinta ya sanar da ita zai je jihar Borno daga Delta don harkokin kasuwancin shi amma sai ganin hotunan sabon auren shi ta yi
- Ta bayyana yadda aurenta na shekaru 9 da shi ya kasance cike da hakuri da wulakancin mahaifiyar shi wacce ta ce ita ke juya su
Wata matar aure a jihar Delta ta bada labarin cin amanar da mijinta wanda suka yi shekaru tara tare yayi mata. Matar mai suna Awele Ejiofor ta bayyana yadda mijinta mai suna Toby Onyekweli ya ce mata zai tafi jihar Borno kasuwancin shi amma sai ganin hotunan auren shi ta yi, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.
Matar cike da matukar kunar rai ta bayyana hakan a shafinta na Facebook. Mijin nata a cikin jihar Delta ya nemi auren kuma aka daura bayan bai sanar da ita ba.
Kamar yadda ta wallafa: "Shekaru tara muka yi tare. Ka tuna lokacin da aka sa mana ranar aure har aka daura a watan Augusta na 2011? Muna rayuwarmu cikin zaman lafiya da hakuri da juna. A haka muka haifa yaranmu muke rainonsu.
KU KARANTA: Kuda wajen kwadayi: Ta auri wani mutumi saboda kudin, daga baya yaje yana hada ta da karenshi yana lalata da ita
"Ka tashi lafiya ranar ka sanar dani zaka je kasuwancinka jihar Borno. Ka sumbaci goshina tare da shiryawa don kada ka yi dare. Ashe shirinka na aurenka ne. Shirin cin amanata ne da tozarta alkawarin aurenmu. Auren shekaru tara cif. Na jure duk wani fadi tashi, na jure wulakancin mahaifiyarka wacce ke juya mu yadda ta so. Ashe da abinda zaka yi min sakayya kenan.
"Mu ba musulmai bane kuma addini da al'adarmu basu amince mu auri mace fiye da daya ba. Ka tozarta rantsuwar aurenka. Akwai ranar sakamako."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng