An sake kwatawa: Yan bindiga sun sace shanu 105 a jahar Filato

An sake kwatawa: Yan bindiga sun sace shanu 105 a jahar Filato

Kwamandan rundunar Soja ta Operation Save Haven, OPSH ya bayyana cewa wasu gungun miyagu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun tarkata shanu 105 daga garin Bisichi na karamar hukumar Barikin Ladi a jahar Filato.

Kwamandan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun rundunar, Ibrahim Shittu, yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Jos, inda yace sai dai sun samu nasarar kwato shanu 32 daga ciki, inji rahoton Daily Nigerian.

KU KARANTA: Yansanda sun halaka masu garkuwa da mutane 2, sun ceto mutum 20 a Kaduna

Shittu yace lamarin ya faru ne a ranar Litinin da yamma, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bin sawun yan bindigan domin kwato sauran shanun da suka yi awon gaba dasu tare da kamasu domin fuskanci hukunci.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar Fulani makiyaya, Miyetti Allah reshen karamar hukumar Barikin Ladi, Alhaji Shuaibu Bayero ya bayyana cewa yan bindigan sun kora dabbobin ne zuwa lardin Fan, cikin karamar hukumar Barikin Ladi.

Malam Bayaro ya cigaba da fadin cewa tuni suka shaida ma Yansandan yankin Barikin Ladi domin daukan matakin daya kamata. Daga nan ya yi kira ga gwamnati da sauran hukumomin tsaro dasu kawo musu dauki don ganin an kwato shanun.

A wani labarin kuma, akalla mutane 8 da wasu gungun yan bindiga suka yi awon gaba dasu a kan titin Kaduna zuwa Zaria a ranar Laraba sun kubuta sakamakon samame da jami’an rundunar Yansandan Najeriya suka kaddamar a kan miyagun.

Haka zalika Yansandan sun ceto wasu mutane uku dake aiki da kamfanin sadarwa na Airtel da aka sace su a ranar Talata, da kuma wasu mutane 9 da aka sace su tun a ranar 14 ga watan Janairu yayin da yan bindiga suka kai ma ayarin motocin Sarkin Potiskum hari.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Kaduna, Yakubu Sabo ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda yace Yansanda sun kashe yan bindiga 2 a yayin samamen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel