Wani attajiri a Najeriya zai kawar da sauro har abada
Ned Nwoko, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar jihar Delta ta Arewa a majalisar wakilai, ya ce ya shirya tsaf da matuka jirgin da za su yi wa Najeriya feshi gabadaya.
A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Nwoko ya ce feshi ne kadai zai kawo karshen sauro a kasar nan tare da tabbatar da fatattakar cutar Malaria ta har abada.
Kamar yadda wani rubutu da aka wallafa a shafinsa na kan shi ya bayyana, za a dau nauyin jami'o'i biyar a nahiyar Afirka da za su yi bincike don habaka riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
"Gidauniyar Ned Nwoko ta shirya tsaf don fatattakar cutar zazzabin cizon sauro a nahiyar Afirka kafin shekarar 2030," rubutun da aka wallafa ya ce.
DUBA WANNAN: Rashawa: Ba zan sassauta wa Abubakar ba - Gwamnan Bauchi
"Mataki na farko na cimma hakan shi ne feshi a Najeriya da sauran kasashen Afirka don kawo karshen sauro a Afirka. Don cimma wannan manufa, za a yi taro da masu ruwa da tsaki kuma za a nada jakadai da jami'ai don hakan." in ji gidauniyar
"Mataki na biyu kuwa shine kirkiro da hanyar kirkiro riga-kafin cutar zazzabin cizon sauron. Gidauniyar Ned Nwoko za ta dau nauyin binciken riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a manyan jami'o'i biyar na nahiyar Afirka." ta kara da cewa.
Nwoko wanda cikin kwanakin nan ya nufa Antarctica, ya ce ya zabi nan ne don ya jawo hankali a kan yakin korar zazzabin cizon sauro a Najeriya da Afirka.
"Babban aiki ne da muka shirya tabbatar da shi. Zaku iya tunanin cewa Najeriya ta yi girman da ba za a iya yi mata feshi ba amma zamu yi kuma za ku gani," in ji shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng