Gwamna Uzodinma zai yi maganin masu garkuwa da mutane da Yahoo-Yahoo

Gwamna Uzodinma zai yi maganin masu garkuwa da mutane da Yahoo-Yahoo

A Ranar Larabar nan ne Mai girma gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya yi alkawari zai yi maganin duk wasu ‘Yan damfara a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa zai yaki Mazambata da ‘Yan damfarar nan wanda ake kira ‘Yan Yahoo-Yahoo da wadanda sa ka addabi jama’a.

Hope Uzodinma ya yi wannan bayani ne a jawabinsa na farko da ya yi wa mutanen jihar Imo jiya bayan ya zama gwamna a makon da ya gabata.

Sanata Uzodinma ya ke cewa zai kafa wasu Dakaru na musamman da za su yi maganin ‘Yan damfara da masu garkuwa da mutane a Imo.

‘Yan Operation Flush Out Criminals da gwamnatin APC za ta kirkira, za su bi ta kan masu aikata laifuffuka iri-iri a jihar Imo inji gwamnan.

KU KARANTA: Ana kashe jama'a na amma an ki daukar mataki - Sanatan APC

Gwamna Uzodinma zai yi maganin masu garkuwa da mutane da Yahoo-Yahoo
Hope Uzodinma ya karbi mulkin Imo bayan hukuncin kotun koli
Asali: Twitter

A jawabin gwamna Uzodinma, ya bada tabbacin kafa wasu Jami’ai na 'North East West.’ da za su rika sintiri a makwabta domin inganta tsaro.

Mai girma Uzodinma, ya ce wannan Runduna da za a kafa, za su yi aiki tare da ‘Yan Sanda, Sojoji, DSS, NSCDC, da sauran jami’an tsaron kasar.

Gwamnan Imo ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da masu kasa da sauran shugabanni da jagororin kungiyoyi su hada-kai da gwamnatinsa.

“Kin bada rahoto ko boye bayani ko amfana daga abin da aka samu wajen aikin laifi zai jawowa mutum mummunan hukunci.” Inji Gwamnan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng