Coronavirus: Bayani game da wata sabuwar cuta da ta barke daga Sin
Akalla mutane 17 su ka mutu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya.
Kawo yanzu akwai mutane 550 da su ka kamu da wannan cuta a fadin Duniya. Mun tsakuro bayanai daga gidan Aljazira game da wannan mummunan cuta.
1. Mecece coronavirus?
Coronovirus ta na cikin dangin cututtuka irin su MERS da SARS da ke kawo matsalar numfashi. Cutar ta saba addabar dabbobi kafin yanzu ta bayyana jikin mutum.
2. Alamun cutar
Alamomin kamuwa da wannan cuta sun hada da:
1. Samun matsalar numfashi
2. Tari
3. Zazzabi
4. Gajeren numfashi
KU KARANTA: Zazzabin Lassa ta na cigaba da buge Likitoci da Marasa lafiya
Wannan cuta ta na iya kai ga haifan ciwon pneumonia na sanyi da kuma matsalar koda da taba huhu. A karshe ta na iya kai ga cutar ajali.
Wannan cuta ba za ta yi irin ta’adin da SARS ta yi a 2002 ba inda mutane 800 su ka mutu. Masana kuma su na ganin ba za ta kai MERS illa ba.
3. Ina ake fama da cutar?
Yanzu wannan cuta ta yi kamari ne a Sin. Bayan nan ta fara shiga kasashe kamar Thailand, Koriya ta Kudu, Taiwan, Jafan da Amurka.
4. Maganin cutar?
Kawo yanzu ba a kirkiro maganin da zai iya warkar da wannan cuta ba. Abin da ake yi shi ne kokarin ganin an hana cutar zagaya Duniya.
5. Daga ina cutar ta fito?
Kwayar cutar Coronavirus ta fara barkewa ne a kasar Sin, amma yanzu haka ana bincike domin gano ainihin daga inda cutar ta fara fitowa.
6. Ina mafita
Ana jiran hukumar WHO ta bada sanarwa game da matakin da za a bi domin takaita yaduwar cutar. A yau ake jiran bayani daga hukumar
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng