Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula

Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula

A yau Alhamis ne Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya karba shugaban jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya na jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A yayin ziyarar da suka kai gidan gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya karbesa tare da sauran shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomi 44 na jihar.

Yayin bikin karbar Bichi tare da sauran jahororin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, Ganduje ya fada musu cewa "wannan jar hula bata dace daku ba."

Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Ganduje ya ce, wannan jar hular ba ta dace da kai ba
Asali: Twitter

Da yake mayar da martani ga Ganduje, Rabiu Suleiman Bichi ya ce, "ni kaina na dade ina jin wani irin yanayi a jikina duk lokacin da na sanya jar hula a kaina."

Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Bichi ya mayar da martanin cewa, "shi yasa nake jin wani irin yanayi a jikina duk lokacin da na sanya jar hula a kaina."
Asali: Twitter

Yayin taron, Ganduje ya yaga jar hula tare da sauya wa Bichi hula mai launin kore.

Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Asali: Twitter

Wannan na kunshe ne a takardar da sakataren yada labarai na Gwamnan, Abba Anwar ya fitar kuma jaridar Solacebase ta samu.

Takaradar ta ce tsohon mai bada shawara na musamman ga Injinay Rabiu Kwankwaso, wasu dalibai da gwamnatin Kwankwaso ta dau nauyin karatunsu, shugabannin jam'iyyu na matakai daban-daban duk sun samu halartar taron da aka yi a gidan gwamnatin.

Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Asali: Twitter

A jawabinsa, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Injiniya Rabiu Suleiman Bichi, ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne sakamakon kiran da Ganduje yayi ga jam'iyyun adawa da 'yan siyasa da su hada kai don kai jihar matakin gaba.

DUBA WANNAN: Sabon salo: 'Yammata da zawarawan arewa sun nemi a fara yi wa maza gwajin hankali kafin aure

"Mun yadda da cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da hankali wajen habaka jihar mu, shiyasa ya gayyaci 'yan adawa da su zo a hada hannu don kai jihar Kano matakin gaba," in ji shi.

Bichi ya jaddada cewa a matsayinsa na tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP kuma shugaban Kwankwasiyya "...a yau mun amsa kiran Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wajen shiga gwamnatin."

Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Ganduje ya karbi shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, ya yaga jar hula
Asali: Twitter

A mayar da martanin da Ganduje yayi, ya ce an karbesu hannu bibbiyu tare da tabbacin cewa za a yi tafiyar habaka jihar Kano da su.

Ya tuna lokacin da suke Kwankwasiyya tare da Bichi inda ya ce sun yi iya kokarinsu wajen ganin habakar siyasar amma sai tafiyar ta sauya salo

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai: Arc. Aminu Dabo, Idris Bello Dambazau, Nasiru Aliko Koki, Bala Gwagwarwa, Tijjani Dambazau da Binta Sipikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel