'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojoji 8 a Borno

'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojoji 8 a Borno

A kalla sojojin Najeriya takwas ne ciki har da mai mukamin laftanant suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu suka jikatta kuma wasu har yanzu ba a gano inda suka ba sakamakon harin da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP suka kai a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Kaga na jihar Borno a ranar Talata kamar yadda majiyar hukumomin tsaro suka ruwaito.

ISWAP sun kai farmaki kauyen Mainok da ke hanyar Maiduguri zuwa Damaturu misalin karfe 1 na rana a karamar hukumar Kaga inda suka bude wa sojojin wuta a yayin da suke haka ramukka don kare sansanin su.

Majiyar tsaron ta kuma ce mayakan na ISWAP sun yi awon gaba da motocci masu dauke da bindiga na bataliya ta 121 amma daga bisani 'yan sanda sun kwato motocin.

Majiyar ta ce, "Ba muyi tsamanin abokan gaba bane domin sun taho a cikin mota mai garkuwa da 'yan sanda suka iso wurin da muke haka rami domin tsare sansanin mu da ke kusa da garin Mainok.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Shugaban masu garkuwa da mutane na Abuja da 'yan kungiyarsa 36 sun mika kansu ga hukuma

"Kwatsam kawai sai suka bude wa sojojin mu wuta, sun kashe guda takwas nan take ciki har da wani laftanant kuma akwai wasu sojojin da har yanzu ba a gano su."

Kazalika, Jami'an 'yan sanda masu yaki da fashi da makami (SARS) a Borno a ranar Talata sunyi nasarar dakile wata harin kwantar Bauna inda suka kashe 'yan kungiyan Boko Haram biyar a kauyen Mainok bayan da suka kai hari a sansanin sojojin.

An ruwaito cewa duk da cewa 'yan ta'addan sunyi musayar wuta da 'yan sandan na SARS, 'yan sandan sun yi galaba a kansu cikin kankanin lokaci.

Wani kwakwarar majiya daga 'yan sanda ya shaidawa Daily Trust cewa kimanin 'yan ta'adda biyar 'yan sandan suka kashe sannan wasu da dama sun tsere da raunin bindiga bayan musayar wutan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel