Tirkashi: Bayan shafe sa'o'i 18 a hanya domin kaiwa saurayinta ziyara, taje ta iske shi da wata budurwar a daki

Tirkashi: Bayan shafe sa'o'i 18 a hanya domin kaiwa saurayinta ziyara, taje ta iske shi da wata budurwar a daki

- Wata budurwa ta wallafa labarin ziyarar da ta kai wa wani saurayinta wacce ta yi da ta sani mai yawa

- Kamar yadda ta ce, saurayin na nesa ne don tafiyar awa 18 ta yi kafin ta kai garin da yake

- Bayan isarta sai ga budurwar shi ta iso wacce ta ce babu inda za ta je, a takaice dai saurayin da budurwar shi suka kwanta a gado inda mai ziyara ta kwanta a kasa

Wata budurwa ta yi bayanin yadda ta sha tafiyar awa 18 don ziyarar saurayinta amma ta tarar da budurwar shi a dakin shi mai ciki daya tak, kamar yadda jaridar Ghana web ta wallafa.

Kamar yadda Seyishae ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani, a ranar dai a kasa ta kwana inda saurayin da budurwar shi suka haye gadon da daddare.

Kamar yadda ta wallafa, "na tuna wata soyayyar nesa da nayi da wani saurayi. Ba ta kare da kyau ba kuwa. Na kai mishi ziyara don awa 18 nayi kafin in isa inda ya ke amma kawai sai ga asalin budurwar shi ta bayyana. Mummunan abinda ya taba faruwa dani kenan a duk rayuwata.

KU KARANTA: Kamar karya: Maza kala-kala matata ke kaiwa gadonmu na sunnah - Miji ya koka

"Maza gaskiya 'yan damfara ne. Ashe a daki mai ciki daya ya ke zama. Budurwar kuwa ta ce ba inda za ta je. Ban da yadda zanyi don ban san ko ina ba balle in tashi in wuce.

"A takaice dai, dole ta sa na kwana a gidan. Sun kwanta a kan gado ni kuwa na kwanta a kasa. Na sha kukan da ya isheni a daren." Cewar kyakyawar budurwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel