Za mu dawo da Diezani Allison Madueke gida Najeriya don ta fuskanci hukunci – Magu

Za mu dawo da Diezani Allison Madueke gida Najeriya don ta fuskanci hukunci – Magu

Shugaban hukumar yaki da rashawa dayi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana manufarsa na ganin hukumar ta kamo tsohuwar ministar man fetir Diezani Allison Madueke don ganin ta fuskanci hukunci a gida Najeriya.

Madueke wanda ta rike mukamin ministar albarkatun man fetir a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na fama da tuhume tuhumen badakala, handama da babakere, da kum cin hanci da rashawa a kanta, amma zakara ya bata sa’a ta tsere zuwa Ingila.

KU KARANTA: Magidanci ya shaida ma kotu yadda matarsa ta hana shi hakkin aure tsawon shekara 1

Magu ya bayyana wannan manufa tasa ce a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu yayin wani ziyarar aiki na kwana daya da ya kai zuwa ofishin hukumar EFCC dake kula da shiyyar Ibadan, inda ya bayyana cewa akwai bukatar hukunta ire irensu Diezani don karfafa yaki da rashawa.

A jawabinsa, Magu yace hukumar ta gano miyagun ayyuka da tsohuwar ministar take da hannu a ciki, tun daga cin amanar mukami, cin hanci da rashawa, zamba, barnatar da dukiyar al’umma, da kum satar kudaden al’umma.

“Don haka ta tsere daga Najeriya don gudun amsa tambayoyi game da wa’adin mulkinta a matsayin minista tare da yadda ta gudanar da aikace aikacen ma’aikatar ta. Duk da cewa na rasa dalilin da yasa kasar da ta gudu suka kasa miko mana ita, amma zamu yi iya kokarinmu don ganin mun kamo ta a shekarar nan.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Yan Najeriya sun yi diran angulu a kan tsohon Sanatan mazabar jahar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye sakamakon yadda yake ma jama’a gadara tare da kwalelen arzikin daya mallaka, arzikin da suka ce nasu ne ya kwasa.

Dino Melaye ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda aka hange shi zaune a kan wata kujerar alfarma cikin wani katafaren gida, ya yi ma hotunan taken; “Kada ku tambaye ni ta yaya, ku tambayi Allah wanda Ya yi mani nasibi. Allah mai girma, girma naka ne, Dino Melaye na godiya a kullum.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel