Dattijan APC sun bayyana matsayarsu a kan zaben maimaici na Kiru/Bebeji

Dattijan APC sun bayyana matsayarsu a kan zaben maimaici na Kiru/Bebeji

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji wanda kotu ta soke zabensa, Abdulmumin Jibrin Kofa ya shiga tsilla-tsilla bayan dattijan APC na jihar Kano sun ce ba zasu goya masa baya ba.

Majiyar gidan rediyon Dabo FM ta bayyana cewa hakan ya fito cikin rahoton jaridar Prime Times ne wanda ta tabbatar da dattawan jam'iyyar zasu yaki Kofa a zaben da za a sake yi a mazabun Kiru da Bebeji na ranar Asabar.

Kamar yadda daya daga cikin dattawan ya bayyana “Kofa bazai samu nasara a zaben da za’a sake na ranar Asabar ba, saboda muna zargin yana yiwa Kwankwaso aiki ne a cikin APC, don haka zamu kayar dashi."

DUBA WANNAN: Shugaban PDP na Kano, Rabiu Bichi ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC

Bayan rikicin da ya barke tsakanin Abdulmumin Kofa da shugaban jam'iyyar APC ta jihar Kano Abbas Abdullahi, a ranar Litinin da ta gabata sunci karo a filin sauka da tashin jiragen sama.

Tuni Abdulmumin Kofa ya durkusa har kasa inda ya gaishesa a filin sauka da tashin jiragen saman da ke Kano.

Bayan wannan, an gano cewa dan majalisar ya garzaya gidan gwamnatin jihar don yiwa gwamna Ganduje murnar nasara a kotu.

Hakazalika, an ga hotunansa da Sanata Kabiru Gaya a garin Abuja. Sai dai kuma ana ganin yana yin ladabin ne don ya samu goyan bayan sake darewa kujerarsa da ke girgidi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel