Sarki Sanusi ya bayyana ainahin abin da ke janyo rikicin addini a Najeriya

Sarki Sanusi ya bayyana ainahin abin da ke janyo rikicin addini a Najeriya

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido II, ya bayyana cewa ba komai ke haddasa rikice-rikicen addini tsakanin Musulmi da Kirista ba a Najeriya illa rashin ilimi wato jahilci.

Sarki Sanusi wanda ya wakilci sarkin Musulmai kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Abubakar Sa’ad a wani taro da ke gudana kan mafita ga rikice-rikicen addini a Najeriya a Abuja, ya ce a tarihi akwai lokacin da Musulmai suka taba zuwa hijira wajen Shugaban kiristoci a kasar habasha.

Mai martaba sarkin ya cigaba da cewa yadda ake watsa labaran karya a shafukan sadarwa na daga cikin abubuwan da ke bunkasa matsalar rikicin addini.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zargin rashawa: Tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke ya isa kotu don gurfanar dashi

Shi ma a nasa jawabin, Rabaran Mathew Hassan Kuka ya ce ya yi kisan jama'ar da ake yi a Najeriya ya isa haka inda ya nemi da a hada hannu a tunkari gwamnati domin ta dakatar da hakan.

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan Reverend Lawan Andimi, wanda ya kasance Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na gida kuma babban fasto a yankin Michika, jihar Adamawa wanda kungiyar yan ta’adda ta yi.

Gwamnonin arewa sun bayyana cewa sun yi bakin ciki matuka kan lamarin.

A wani jawabi a Jos a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu, Shugaban kungiyar gwamnonin arewan kuma Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong ya bayyana lamarin a matsayin wani abun bakin ciki na rashin imani daga kungiyar yan ta’addan wacce ta yi kaurin suna wajen sanya radadi a zukatan yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel