Kwankwasiyya Vs Gandujiyya: Komawan Rabiu Bichi APC bai ragemu da komai ba - Sakataren PDP a Kano

Kwankwasiyya Vs Gandujiyya: Komawan Rabiu Bichi APC bai ragemu da komai ba - Sakataren PDP a Kano

Sakataren jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa fitar shugabansu, Dakta Rabiu Sulaiman Bichi, ba zai cutar da su ko da kwayar zarra ba.

Sagagi yayinda yake hira da Daily Trust ranar Talata ya bayyana cewa jam'iyyar za ta cigaba da tafiya da duk wanda ke shirye da taimaka mata wajen cigaba.

Ya ce jam'iyyar PDP bata samu wasika daga Dakta Suleiman Bichi, kan komawarsa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba amma lallai tsohon shugaban nasu ya bayyana masa niyyar barin jam'iyyar

Yace: "Lallai, Dakta Bichi ya sanar da ni niyyarsa na fita daga PDP, amma bai sanar da jam'iyya ba. Saboda hakan, PDP har yanzu tana sauraronsa ya rubuto wasikar fita. Yana da hakkin bin ra'ayinsa."

Shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, a jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi ya raba jiha da tsohon amininsa, Rabiu Kwankwaso.

Mun rahoton cewa Bichi wanda ya rike muƙamin sakataren gwamnatin jihar Kano daga 2011 zuwa 2016, zai sanar da komawarsa jam'iyyar APC tare da magoya bayansa a ranar Laraba.

Majiya na kusa da shugaban jam'iyyar ta ce ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar tun kafin hukuncin kotun kolin na tabbatar da Abdullahi Ganduje a matsayin hallastastaccen zaɓaɓɓen gwamna.

"Ficewar Rabiu Sulaiman Bichi daga PDP ba ta da alaƙa da hukuncin kotun ƙoli sai dai saboda wasu aƙidu da dalilan da basu shafi siyasa ba," a cewar wani na kusa da shi da ya nemi a sakayya sunansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel