Magidanci ya shaida ma kotu yadda matarsa ta hana shi hakkin aure tsawon shekara 1

Magidanci ya shaida ma kotu yadda matarsa ta hana shi hakkin aure tsawon shekara 1

Wani magidanci dan kasuwa, Malami Abdullahi ya bayyana ma kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa yadda matarsa Fatima ta hana shi daman kwanciya da ita tsawon shekara 1.

Abdullahi mazaunin unguwar Rigasa ya bayyana ma kotun a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu cewa matarsa tana neman maza, baya ga hana shi hakkinsa na kwanciyar aure, amma duk da haka yana son abin sa.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Miyagu sun kai hari jahar Nassarawa, sun kashe mutane 4

“Ina son ta haka, kuma ina rokon kotu ta warware matsalar dake tsakaninmu da ita, tare da hanata bukatarta na kashe auren. A gaban take daukan wayoyin wasu mazan, don haka na turata gidansu don ta koyi zaman aure. Na sha kai ta kara wajen iyayenta, sai dai su yi ta bani hakuri, kuma a haka nake mayar da ita.” Inji shi.

Sai dai tun a farkon zaman, lauya mai shigar da kara a madadin matar, Adamu Garba ya bayyana ma kotun cewa Fatima tana neman kotu ta kashe auren ne saboda duka da cin zarafi da Abdullahi yake mata.

“Yana yawan dukanta, ya koreta daga gidansa zuwa gidan iyayenta har sau hudu, na karshe da aka yi har da saki ya hada mata, amma daga bisani ya mayar da ita. Rokon da muke ma kotu shi ne ta kashe auren gaba daya saboda ba za ta iya zama da shi ba.” Inji shi.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin kotun, mai sharia Muhammad Adam-Shehu ya nemi ma’auratan su sasanta kansu zuwa ranar 6 ga watan Feburairu, idan kuma bai yiwu ba, kowa ya gabatar da iyayensa gaban kotu a ranar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel