Tashin hankali: Tsananin sanyi na kashe mutane a kasar Afghanistan

Tashin hankali: Tsananin sanyi na kashe mutane a kasar Afghanistan

- Saboda zubar dusar kankara da ta tsananta a jihar Logar da ke Afganistan, mutane biyar sun sankare inda suka mutu har lahira

- Mutane biyar din suna zama ne a sansanin masu neman mafita da ke jihar Logar din

- Didar Ahmad Lavang ya bayyana cewa an dakatar da fita tare da wasu lamurran rayuwa a wasu gudumomi na jihar Logar din

Sakamakon zubar dusar kankara da ta tsananta a jihar Logar da ke Afganistan, mutane biyar da ke wani sansanin masu neman mafaka sun rasa rayukansu.

Didar Ahmad Lavang, kakakin fadar gwamnan Logar ya ce tsawon kwanaki ana ta ruwan dusar kankara a jihar wanda hakan ya janyo sanyi mai tsanani.

Lavang ya kara da cewa sakamakon tsanantar sanyin ne mutane biyar da ke sansanin masu neman mafakar suka mutu saboda tsanantar da halin ya yi.

Ya ce saboda tsanantar sanyin ne aka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a gundumoni da dama na Logar, kamar yadda jaridar TRT ta kasar Turkiyya ta ruwaito.

Idan zamu tuna, sanyin Najeriya da ma kasashen yammacin nahiyar Afirka da dama ya tsananta a lokacin sanyin nan, lamarin da masana ilimin muhalli suka dangana da lamurran jama'a da ke shafar muhalli.

KU KARANTA: PDP na hada makarkashiya da 'yan majalisa domin su tsige ni - Sabon Gwamnan Imo

A farkon watan Janairu din nan ne aka tashi a jihar Kano da wani sanyi mai tsanani, inda har sanyin garin ya kai 8 celsius kasa da na birnin London a ranar wanda ya kai 11 Celsius.

Ba jihar Kano kadai wannan sanyin ya ta'azzara ba, mazauna jihar Jos sun koka da yadda sanyin ya ta'azzara. A jihohi da yawa na Najeriya mutane sun dena fita sana'o'i da sauran harkokin rayuwarsu saboda tsanantar sanyin.

Abin farin ciki kuwa a lokacin shi ne yadda yara 'yan makaranta ke hutu, amma da iyaye da yawa ba zasu bar su fita a cikin wannan sanyin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel