Wata mata ta doke fasto, bayan ya bayyana cewa mata masu kiba baza su shiga aljannah ba

Wata mata ta doke fasto, bayan ya bayyana cewa mata masu kiba baza su shiga aljannah ba

- A coci dai an san fastoci da bayani tare da warware matsalolin da suka shafi addini da kuma rayuwa

- Wani fasto a kasar Brazil ya hadu da fushin wata mata bayan ya ce mata masu kiba ba zasu shiga aljanna ba don kuwa bankado shi tayi daga kan mimbari

- Tuni 'yan sanda suka kamata amma an sanar dasu cewa bata da isasshen hankali a tare da ita

A coci dai an san fastoci da bayani tare da huduba ga jama'a. Sau da yawa hudubobin kan tabo addini ne tare da wasu manyan lamurran da ke ci wa mutane tuwo a kwarya. Amma ba abin mamaki bane idan hankalin mutum ya dauku a kan wani abu daban a yayin da ake hudubar. Hakan ne kuwa ya faru da wani fasto a kasar Brazil.

Kamar yadda bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna, wata mata ta dira gaban faston inda ta bankado shi daga kan mimbarin cocin bayan da yayi katobara yayin huduba.

Rahotanni sun nuna cewa fasto Marcelo Rossi sanannan fasto ne na cocin katolika da ke Cancao Nova a Brazil.

Lamarin ya bar mutane cikin dimuwa don ba zasu iya bayyana takamaiman abinda ya faru ba a kan mimbarin. An ga daruruwan masu bauta sun tashi daga wajen zamansu bayan fasto ya fadi kasa.

KU KARANTA: An nemi Uban ango da Uwar amarya an rasa, yayin da ake saura kwanaki kadan daurin aure

Bayan faduwar shi, Rossi ya ce: "kada ku damu, lafiyata kalau. Babu abinda ya faru dani."

Bayan nan faston bai kara wata magana mai kawo rudani ba kuma a bidiyon an ga yadda masu bautar suka rude.

'Yan sanda sun hanzarta kama matar amma daga bisani kawarta ta ce bata da isasshen hankali. Saboda bai ji ciwo ba kuma bai bukaci a hukunta matar ba, sai aka saketa, kamar yadda jaridar IndiaTimes ta ruwaito.

Daga bisani dai an gano cewa fasto katobara yayi a cocin inda ya ce mata masu kiba ba zasu shiga aljanna ba. Wannan lamarin ne ya fusata matar har ta banko shi daga kan mimbarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel