Shugaban PDP na Kano, Rabiu Bichi ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC

Shugaban PDP na Kano, Rabiu Bichi ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC

Shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, a jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi ya raba jiha da tsohon amininsa, Rabiu Kwankwaso.

Daily Nigerian ta samu ingantaccen rahoton cewa Bichi wanda ya rike muƙamin sakataren gwamnatin jihar Kano daga 2011 zuwa 2016, zai sanar da komawarsa jam'iyyar APC tare da magoya bayansa a ranar Laraba.

Majiya na kusa da shugaban jam'iyyar ta ce ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar tun kafin hukuncin kotun kolin na tabbatar da Abdullahi Ganduje a matsayin hallastastaccen zaɓaɓɓen gwamna.

"Ficewar Rabiu Sulaiman Bichi daga PDP ba ta da alaƙa da hukuncin kotun ƙoli sai dai saboda wasu aƙidu da dalilan da basu shafi siyasa ba," a cewar wani na kusa da shi da ya nemi a sakayya sunansa.

DUBA WANNAN: An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina (Hotuna)

"A baya-bayan nan an mayar da Rabiu Bichi saniyar ware a harkokin tafiyar Kwankwasiyya duk da irin gudunmawa da ya ke bayarwa ana masa kallon mai hana ruwa gudu."

Wannan shine sabon baraka da aka samu a tafiyar Kwankwasiyya tun bayan ficewar tsohon mataimakin gwamna, Hafiz Abubakar, tsohon manajan NPA, Aminu Dabo da wasu da suka fice daga jam'iyyar gabanin babban zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel