Zamu dawo da duk mabarnatan da suka gudu turai suka buya - Magu
Makaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa hukumarsa zata nemi a dawo da duk wasu mabarbata dukiyar jama'ar Najeriya da suka turai suka buya.
Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake gana wa da manema labarai a ofishin shiyyar hukumar na Ilorin.
Magu, wanda ya kai ziyarar aiki jihar Kwara, ya bayyana cewa an shigo sabuwar shekara, a saboda haka hukumar EFCC ta sabunta yakin da take yi da karya tattalin arziki kuma za a gurfanar da duk wanda aka samu da alifi.
"Zamu gayyaci da duk wanda muke bincike, sannan mu gurfanar da shi a gaban kotu da zarar mun kammala bincike.
"Wannan somin tabi ne, zamu nemi a dawo da mabarnata da dama da suka gudu turai suka buya, basu tsira ba don kawai suna zaune a kasashen ketare.
"Tamkar yanzu muka fara yaki da cin hanci, mun fito da karfinmu a sabuwar shekaru," a cewar Magu.
Kazalika, Magu ya yi watsi da zargin cewa hukumar EFCC tana farautar wasu zababbun mutane ne.
"Ba gaskiya bane, jihar Kwara ta cancanta ta samu hedikwatar EFCC saboda tana daya daga cikin tsofin jihohi a kasar nan. Ba don wani muka kawo ofishinmu nan, mun kawo shi don kowa da kowa," kamar yadda Magu ya bayyana.
A ziyarar da yake yi a kasar Ingila, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nemi kasar ta dawo da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke, gida Najeriya domin ta fuskanci tuhumar da hukumar EFCC ke yi a kan laifan cin hanci da barnatar da dumbin dukiyar Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng