Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda yan sanda suka kara da yan Shi’a a Abuja

Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda yan sanda suka kara da yan Shi’a a Abuja

- Mutum guda ya rasa ransa yayinda yan Shi'a suka kara da yan sanda a Abuja

- An tattaro cewa lamarin ya afku ne a lokacin da yan sanda ke harbi on tarwatsa mabiya Shi'an da ke zanga-zanga a birnin tarayyar

- An ruwaito cewa masu tafiya da kafa da sauran jama’a sun ci na kare a lokacin da lamarin ya afku

Rahotanni sun kawo cewa an kashe wani mutum guda da ke wucewa yayinda yan sanda ke harba bindiga da borkonon tsohuwa don tarwatsa wani zanga-zanga da yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wato shi’a ke yi a Yankin Berger da ke Wuse a Abuja.

Hargitsin ya yi sanadiyar kawo karshen tattakin wanda ya fara daga Utako.

Wani idon shaida ya fada ma majiyarmu ta The Nation cewa masu tafiya da kafa da sauran jama’a sun ci na kare a lokacin da lamarin ya afku.

An tattaro cewa yan sanda sun dauke gawar mutumin da aka kashe.

Yan Shi’an dai na neman a saki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat wadanda gwamnati ta tsare a wani gidan kurkuku da ke jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kama masu amfani da kakin soji wajen garkuwa da mutane a Kaduna (Hoto)

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yan sandan da ke kasa basu da niyar yin sharhi kan lamarin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel