Atiku ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a jihohin arewa 4

Atiku ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a jihohin arewa 4

A ranar Talata ne kotun koli ta yi watsi da bukatar jam'iyyar APC da 'yan takararta dake kalubalantar nasarar gwamnonin jam'iyyar PDP a jihohin Adamawa, Bauchi, da Benuwe.

A ranar Litinin ne kotun kolin mai alkalai 7 a karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta tabbatar wa da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, nasarar da ya samu.

A wani takaitaccen sako da ya fitar ranar Talata jim kadan bayan sanar da hukuncin da kotu ta zartar a kan kujerun gwamnonin jam'iyyar PDP na jihohin Adamawa, Bauchi da Benuwe, Atiku ya jinjina wa 'yan Najeriya tare da taya gwamnonin murna.

Atiku ya yi magana a kan hukuncin kotun koli a jihohin arewa 4
Atiku
Asali: Twitter

"Ina mai jinjina ga 'yan Najeriya bisa jazircewarsu sannan ina taya Gwamna Samuel Ortom, Gwamna Ahmed Fintiri, Sanata Bala Mohammed da Aminu Waziri Tambuwal, a kan nasarar da suka samu a kotun koli," kamar yadda Atiku ya rubuta cikin harshen Turanci.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya bude kamfanin sutura

A makon jiya ne Atiku ya shawarci tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, da ya rungumi kaddara a kan hukuncin da kotun ta zartar na karbe kujerarsa tare da mika ta hannun Sanata Hope Uzodinma, dan takarar jam'iyyar APC.

Atiku ya sanar da Ihedioha cewa kotun koli ce karshe a bangaren shari'a a Najeriya, a saboda haka ba zai iya kalubalantar hukuncin data yanke ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel