Akwai shingen tsare ababen hawa na 'yan Boko Haram a kan hanyar zuwa Maiduguri - Rundunar soji

Akwai shingen tsare ababen hawa na 'yan Boko Haram a kan hanyar zuwa Maiduguri - Rundunar soji

Rundunar sojojin Najeriya ta magantu a kan dawowar sabbin hare - haren mayakan kungiyar Boko Haram a kan babban titin Damaturu zuwa Maiduguri.

Kwamandan atisayen 'Ofireshon Lafiya Dole', Manjo Janar Olusegun Adeniyi, ya ankarar da direbobi da sauran masu ababen hawa a kan shigayen tsare ababen hawa na bogi da 'yan Boko Haram suke saka wa a kan hanyar Damataru zuwa Maiduguri.

Adeniyi ya gargadi direbobi da kada su tsaya a kowanne shingen binciken ababen hawa bayan wadanda suka sani na rundunar sojin Najeriya dake garin Benisheikh, Jakana, Auno, Mainok da Njimtilo a kan hanyar zuwa Maiduguri.

Manjo Janar Adeniyi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a hedikwatar atisayen 'ofireshon lafiya dole' dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Akwai shingen tsare ababen hawa na 'yan Boko Haram a kan hanyar zuwa Maiduguri - Rundunar soji
Buratai da Farfesa Zulum
Asali: Facebook

Ya alakanta dawowar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a kan hanyar da rashin samun nasarar kama wani gari domin kafa daularsu.

Kazalika, ya kara da cewa mayakan na amfani da mutanen da suka kama wajen yi musu noma da bautar dasu da aiyuka masu wahala a maboyarsu.

DUBA WANNAN: Aminu Dorayi: Farfesan Najeriya da ya tuko mota tun daga Ingila har zuwa Kano

A ranar Litinin ne rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen kasashen ketare a kan shiga lamurran da suka shafi tsaron kasar nan ballantana yaki da Boko Harama da kuma ISWAP.

Duk da rundunar sojin ba ta sanar da sunayen cibiyoyin ba, ta shawarci cibiyoyin gida da na wajen da su kiyaye wajen goyon bayan kungiyoyin ta’addancin.

Amma kuma ta jaddada cewa ana ci gaba da yakar ta’addancin da ya yi katutu a yankin Arewa maso gabas, ko kuma sauran bangarorin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel