Gwamna Zulum ya yi tattaki zuwa Chadi, ya gana da rundunar kasa da kasa

Gwamna Zulum ya yi tattaki zuwa Chadi, ya gana da rundunar kasa da kasa

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ziyarci hedkwatar tsaro na hadin gwiwar kasa da kasa a N’Djamena, babbar birnin kasar Chadi.

Rundunar tsaron wadanda mafi akasarinsu daga kasashen Chadi, Kamaru, Nijar da Najeriya suka fito, sun kasance da hannu wajen yakar yan ta’addan Boko Haram a tafkin Chadi, wanda wasun su ke a yankin arewacin jihar Borno da garuruwan sauran kasashen.

Zulum, wanda ya bar filin jirgin sama na Maiduguri a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu ya isa Chadi gabannin aiwatar da ayyukansa.

Gwamna Zulum ya yi tattaki zuwa Chadi, ya gana da rundunar kasa da kasa
Gwamna Zulum ya yi tattaki zuwa Chadi, ya gana da rundunar kasa da kasa
Asali: UGC

Kwamandan rundunar hadin gwiwar, Manjo Janar I.M. Yusuf ne ya tarbi Zulum a hedkwatarsu.

Mambobin majalisar dokokin jihar wadanda mazabunsu ke a yankunan da abun ke gudana ne suka yiwa Gwamna Zulum rakiya. Hakazalika sakataren gwamnatin jihar da wasu kwamishinoni biyu da jami’ai na a tafiyar.

Zulum da kwamandan rundunar sun yi ganawar sirri kan yaki da Boko Haram a yankunan jihar Borno. Sai dai ba a bayyana cikakken bayanin ganawar ba saboda dalilai na tsaro.'

KU KARANTA KUMA: Akwa-Ibom: Akpabio bai isa ya janye daga takarar Sanata ba – INEC

A taron, Janar Yusuf ya jinjinawa ziyarar da Zulum ya kawo masu wanda hakan ke nuna jajircewarsa wajen ganin ya gina zaman lafiya a Najeriya da sauran kasashen da abun ya shafa.

Gwamna Zulum ya yi godiya ga rundunar kan jajircewarsu, sannan ya basu tabbacin samun goyon bayansa a koda yaushe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel