Akwa-Ibom: Akpabio bai isa ya janye daga takarar Sanata ba – INEC

Akwa-Ibom: Akpabio bai isa ya janye daga takarar Sanata ba – INEC

Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ta yi magana game da yunkurin Sanata Godswill Akpabio na janye kansa daga takarar Sanata a zaben Akwa Ibom.

INEC mai zaman kanta, ta ce Godswill Akpabio ne zai sake tsayawa jam’iyyar APC a matsayin ‘Dan takara a zaben da za yi a Ranar 25 ga Watan Junairun 2020.

Godswill Akpabio wanda yanzu ya zama Minista a gwamnatin shugaban kasa Buhari ya nemi INEC ta maye gurbinsa da wani ‘Dan takarar da zai rikewa APC tuta.

Hukumar ta bayyana cewa Ministan ya makara wajen gabatar da bukatarsa, domin kuwa a lokacin da ya nemi a sauya sunansa, lokacin da aka ware, ya riga ya kure.

A wata wasika da ta aiko, INEC ta ce a tsarin dokar Najeriya, ana shiga zaben cike-gurbi ko na karashe ne da jerin ‘Yan takara da jam’iyyun da aka soma zaben da su.

KU KARANTA: Wike ya yi farin ciki da nasarar Gwamnan Sokoto a kotun koli

Akwa-Ibom: Akpabio bai isa ya janye daga takarar Sanata ba – INEC
INEC ta ce babu damar maye gurbin Akpabio da Ekperikpe Luke Ekpo
Asali: Facebook

“Wasikarka wanda aka rubuta a Ranar 10 ga Watan Disamban 2019, inda ka bukaci a maye gurbinka da Hon. Ekperikpe Luke Ekpo a matsayin ‘Dan takarar APC, bayan kotu ta bukaci a sake zabe, ba za ta samu karbuwa ba. Godswill Akpabio ne ‘Dan takaran APC."

A wannan wasika da Sakatariyar hukumar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sa wa hannu, ta ce Godswill Akpabio ne zai rikewa APC tuta a zaben Arewacin Akwa Ibom.

Tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya hakura da kujerar Sanata ne bayan ya zama Ministan Neja-Delta. Wannan ya sa ya ke neman kujerar ta koma hannun Luke Ekpo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel