Zan cigaba da garkame iyakokin shigowa kasarmu – Shugaba Buhari
Mun samu labari a cikin farkon makon nan cewa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ba za a bude iyakokin shiga Najeriya ta kasa ba tukuna.
Buhari ya ce sai lokacin da kwamitin da aka kafa domin duba lamarin iyakokin, ya kammala bincikensa, ya kawo rahoto sannan za ayi la’akari da kiran.
Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a jiya Ranar Litinin, 20 ga Watan Junairu, 2020, wajen wata ganawa da ya yi da Firayim Ministan kasar Birtaniya.
Nana Akufo-Addo da kasar Ghana ya na cikin wadanda aka yi wannan zama da su a taron sha’anin kasuwancin da kasashen Afrika da kuma Birtaniya.
Buhari ya bayyana cewa ba don shinkafa kurum aka garkame wasu iyakokin kasar ba, sai dai don ana shigo da wasu kaya cikin kasar Najeriya ta bayan fage.
KU KARANTA: Buhari ya mikawa Kasar Ingila kokon bararsa a taron Afrika

Asali: Depositphotos
A cewar Shugaban Najeriyar, ana fasa kaurin kayan makamai da mugayen kwayoyi ta iyakoki kasar don haka ya dauki matakin rufe su na wani lokaci.
Muhammadu Buhari ya ce ba zai iya cigaba da zura idanu ya na ganin ana lalata rayuwar Matasa da miyagun kwayoyi tare da gurbata tsaron kasar da makamai.
“A mafi yawan lokacin da aka kama motocin da ke dauke da shinkafa da sauran kayan abinci, za ka samu miyagun kwayoyi da kananan makamai a cikinsu.”
Shugaba Buhari ya nuna takaicinsa na yadda rufe iyakokin ya kawowa tattalin arzikin makwabtan Najeriya matsala, amma ya nuna hakan ya zama dole.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng