Lamari ya ta’azzara: Duk wanda suka zalunce mu Allah Ya tsine musu albarka – Kwankwaso

Lamari ya ta’azzara: Duk wanda suka zalunce mu Allah Ya tsine musu albarka – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jahar Kano, madugun darikar siyasar Kwankwasiyya kuma jigon jam’iyyar PDP a jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya mayar da martani game da hukuncin kotun koli game da zaben gwamnan jahar Kano, inda ya fara da tofin Allah tsine.

Wannan shi ne karo na farko da aka jiyo madugun Kwankwasiyya yace wani abu game da hukuncin kotun kolin, inda aka jiyo shi cikin wani bidiyo yana tsinuwa ga duk wadanda suka sa hannu cikin zaluntarsa, kamar yadda shafin Dokin Karfe ya dauko bidiyon.

KU KARANTA: PDP na yunkurin kifar da gwamnatin Buhari – sabon gwamnan APC

A cewar Kwankwaso; “Kana shan tsinuwa, ko mutum ba’a tsine masa ba, ballantana kullum muna cikin tsine masa, ko yanzu ma ina cewa duk wa’anda suka zalunce mu dana gida, dana waje Allah Ya tsine musu albarka.” Sai jama’an dake wajen suka dauka da “Amin”

Kwankwaso ya cigaba da fadin; “Domin sun mana zalunci, sun zalunci mutan Kano, kuma zamu cigaba da tsine musu albarka damu da yayanmu da jikokinmu daga nan har abada. Sun lalata dimukradiyya, sun shiga cikin harkar sharia sun lalata ta.”

Idan za’a tuna a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu ne ma shairia Sylvester Nguta na kotun koli ya sanar da hukuncin koli game karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jahar Kano, Abba Yusuf ya shigar da Gwamna Ganduje.

Da yake yanke hukuncin, Nguta ya bayyana karar da Abba da PDP suka shigar a matsayin mara tushe balle makama, don haka ya bayyana Ganduje a matsayin halastacce kuma zababben gwamnan jahar Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel