Buhari: Najeriya ta na neman a dawo da ‘Yan kasar ta da su ka yi laifi su ka tsere

Buhari: Najeriya ta na neman a dawo da ‘Yan kasar ta da su ka yi laifi su ka tsere

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci hadin-kan kasar Birtaniya wajen ganin an dawo da ‘Yan kasarsa da su ka aikata laifi, su ka ruga kasa wajen.

Muhammadu Buhari ya yi wannan roko ne a lokacin da ya gana da Firayim Ministan kasar Birtaniya, Boris Johnson a wani zama da su ka yi a taron jiya.

Shugabannin kasashen sun gana ne wajen taron harkar kasuwanci na Birtaniya da kasashen Afrika na wannan shekara wanda aka fara Rana 20 ga Junairu.

A cewar Mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Femi Adesina, Najeriya ta na bukatar hadin-kan kasar Ingila wajen kokarin da ta ke yi na yaki da barayi.

Irinsu Diezani Alison-Madueke da wasu mutanen Najeriya da ake zargi da aikata laifi sun labe a Ingila da sauran kasashen Turai kafin hawan Buhari kan mulki.

KU KARANTA: Ingila ta na maraba da kowa duk da barin kungiyar EU - PM

Buhari: Najeriya ta na neman a dawo da ‘Yan kasar ta da su ka yi laifi su ka tsere
Shugaba Buhari ya roki Ingila ta dawo da marasa gaskiyan Najeriya
Asali: UGC

Buhari ya fadawa Firayim Ministan inda gwamnatinsa ta kwana da irin cigaban da ta samu a bangarori dabam-daban bayan darewarsa kan kujerar mulki.

Mu na da dogon tarihi da Sojin kasar Birtaniya, kuma mu na hada-kai, inji Buhari. A game da sauyin yanayi kuma, Buhari ya yi magana game da tafkin Chadi.

Haka zalika Shugaba Buhari ya shaidawa Boris Johnson cewa Najeriya ta na samun cigaba a wajen harkar ilmi, musamman bangaren karatun Mata a Najeriya.

A jawabinsa, Firayim Ministan ya yabawa Buhari wanda ya kira shugaban Yankinsa saboda aikin da ya ke yi a Afrika, tare da ba shi kwarin gwiwar kara kokari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng