'Yan Najeriya sun fi son daukar hoto dani fiye da tambayar kudi a wurina - Dangote

'Yan Najeriya sun fi son daukar hoto dani fiye da tambayar kudi a wurina - Dangote

- Aliko Dangote, hamshakin mai kudin Afirka ya ce in ya ci karo da 'yan Najeriya basu tambayar shi kudi sai dai hoton selfie

- Ya bayyana cewa ya kan tuka kan shi don ganin gari a duk kwanakin karshen mako a birnin Legas dake kudancin kasar nan

- Dangote ne mafi arziki na 95 a duniya kamar yadda Bloomberg Billionaires Index na 2019 ya bayyana

Aliko Dangote, hamshakin mai kudin Afirka ya ce in ya hadu da 'yan Najeriya, bukatarsu hoto kawai da shi a maimakon su tambaye shi kudi.

Dangote ya sanar da hakan ne a hirar da aka yi dashi a kan rayuwar shi, dukiyar shi da kuma shirin shi a nan gaba wacce David Rubeinstein a wani shirin gidan talabijin da shi David Rubeinstein ke yiwa mutane tambayoyi. Ya ce ya kan tuka kan shi ya zagaye birnin Legas da kan shi a ranakun karshen mako.

Kamar yadda jerin sunayen manyan masu kudin duniya na Bloomberg Billionaires Index ya nuna, Dangote ne mutum na 95 mafi kudi a duniya. Ya ce 'yan Najeriya kan bukaci su yi hoton selfie ne a maimakon tambayar shi kudi.

"Mutane ba su tambayata kudi idan na fito yawon shakatawata cikin ranakun mako amma su kan bukaci mu yi hoton selfie," in ji shi.

KU KARANTA: Tsautsayi ba a sa maka rana: Zakara ya kashe wani mutumi

A wannan tattaunawar ne ya bayyana cewa ana cigaba da gina matatar man fetur din shi wacce za ta kasance mafi girma a duniya kuma za ta dinga sarrafa ganga 650,000 na danyen mai a kullum. Za a kaddamar da matatar ne a watan Janairu na 2020.

Dangote dai shi ne shugaban kamfanonin Dangote Group wadanda suke kasuwancin man fetur, siminti da sauransu a Najeriya da wasu kasashen Afirka.

Yana da arzikin da ya kai dala biliyan 15 a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel