Aminu Dorayi: Farfesan Najeriya da ya tuko mota tun daga Ingila har zuwa Kano

Aminu Dorayi: Farfesan Najeriya da ya tuko mota tun daga Ingila har zuwa Kano

Farfesa Aminu Mohammed Dorayi dattijo ne kuma shahararre a bangaren harkar koyarwa, ya yi karatun digirinsa na farko a jami'ar ABU Zaria a bangaren kimiyya (Chemistry).

Ya shugabanci hadaddiyar kungiyar dalibai (SUG) reshen jami'ar ABU a zangon karatu na 1966/1967.

Farfesa Dorayi ne ya kafa rukunin gidajen masana'antun dake unguwar Saharada a Kano, sannan shine mutum na farko da ya fara shirya kasuwar bajakoli a fadin Najeriya.

Ba iya wadanan abubuwan bajinta ne suka sa Farfesa Dorayi ya fita daban ba, ya kafa tarihi a duniya a matsayin mutum na farko a duniya da ya taba yin tafiya mafi nisan zango da mota bayan ya tuko motarsa, kirar fijo 504, tun daga birnin Landan har zuwa birnin Kano.

Farfesa Dorayi ya kammala tafiyar, mai nisan kilomita 6437.376 (4000miles), a cikin kwanaki 24.

An haifi Farfesa Aminu Mohammed Dorayi a Kano a ranar 16 ga watan Nuwamba, 1942. Mahaifinsa ma'aikacin asibiti ne ya yi aiki tare da Turawa. Mahaifinsa tare da wasu Turawa suka kafa tsohon asibitin garin Kano mai suna 'Kano City Hospital'.

Zama da Turawa ya taimaki mahaifin Farfesa Dorayi, domin hakan ne yasa shi tura dukkan 'ya'yansa zuwa makarantar boko a wancan lokacin.

Aminu Dorayi: Farfesan Najeriya da ya tuko mota tun daga Ingila har zuwa Kano
Farfesa Aminu Dorayi
Asali: Twitter

A saboda haka, Farfesa Aminu Dorayi da sauran dukkan 'yan uwansu sun samu ilimin boko cikin sauki saboda a lokacin ana kyamarsa.

Farfesa Aminu Dorayi ya fara karatun a makarantar firamare ta 'Kano City', wacce ke cikin birnin Kano.

DUBA WANNAN: Mahaifin Sulaiman ya gindaya wa Ba Amurkiyar data zo auren dansa sharudda guda 4

"Makarantun firamare hudu ne kawai a kaf cikin birnin Kano a wancan lokacin; akwai daya a fadar sarki, daya a kusa da gidan Alhassan Dantata, daya a Shahuci (wacce na halarta) da kuma daya a Gidan Makama da kuma wata a Tudun Wada. Babu makarantu da yawa a lokacin, saboda masu zuwa makaranta a wancan lokacin basu da yawa," a cewar Farfesa Aminu Dorayi.

Bayan ya kammala karatun Firamare a Kano, Farfesa Aminu ya wuce kwalejin fasaha (wacce aka sauya wa suna kwalejin gwamnati) ta Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng