Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da zaben Gwamna Muhammed na jihar Bauchi

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da zaben Gwamna Muhammed na jihar Bauchi

- Kotun koli ta jadadda Bala Muhammed na jam’iyyar Peoples Democratic Party a matsayin zababben gwamnan jihar Bauchi

- Kotun ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mohammed Abubakar ya shigar

- Ta ce wanda ke karar ya gaza tabbatar da kuskuren da ke tattare da binciken kotun zaben gwamna na jihar Bauchi da kuna kotun daukaka kara a Jos

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Bala Muhammed na jam’iyyar Peoples Democratic Party a matsayin zababben gwamnan jihar Bauchi.

Ta yi watsi da kara mai lamba SC/1502, wacce tsohon gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mohammed Abubakar ya shigar, inda ya ke kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar.

Jastis Mohammed Dattijo wanda ya yanke hukuncin, ya bayyana cewa wanda ke karar ya gaza tabbatar da kuskuren da ke tattare da binciken kotun zaben gwamna na jihar Bauchi da kuna kotun daukaka kara a Jos.

KU KARANTA KUMA: Kotun koli: Murna ta barke a kan nasarar Ganduje a Kano

Sauran mambobin kwamitin na mutum bakwai sun amince da hukuncin.

A wani labarin kuma mun ji cewa, Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kano na 2019, ya yi martani ga hukuncin kotun koli, wacce ta tabbatar da zaben Abdullahi Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar.

A wani hukunci da Justis Nwali Ngwuta a madadin kwamitin alkalai na mutum bakwai, kotun kolin ta ce karar da Mista Yusuf ya shigar bata da karfi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa a wani jawabi daga kakakin dan takarar gwamnan na Kano, Sanusi Dawakintofa, Mista Yusuf ya yi zargin cewa bangaren shari’a ta yi wasa da damokradiyyar Najeriya wajen yiwa mutanen Kano fashin kuri’unsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel