Hukuncin kotun koli: Ganduje ya yi kira ga abokan adawa da su hada hannu da gwamnatin APC

Hukuncin kotun koli: Ganduje ya yi kira ga abokan adawa da su hada hannu da gwamnatin APC

Yan mintuna kadan bayan hukuncin kotu da ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, gwamnan ya yi kira ga masu adawa da su zo su hada hannu don cigaban jihar.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi dauke da sa hannun babban sakataren labaran gwamnan, Malam Abba Anwar.

“Mun gode ma Allah kan nasararmu a kotun koli wacce ta sake tabbatar damu bayar kotun zabe da kotun daukaka kara. Sannan muna godiya ga mutanen Kano a kan yadda suke gudanar da harkokinsu cikin lumana,” inji Ganduje.

Ya kuma yi godiya da dukkanin mutanen da suka yi addu’a’ idon samun nasarar sa, inda ya jadadda cewa “duk wanda ya yarda sannan ya dogara ga Allah, zai ga haske a farko, tsakiya da kuma karshen lamarinsa a kowani yanayi.

“Sannan mun yaba na dukkanin alkalan da suka kasance a cikin wannan shiri na zurfafa damokradiyya. Wannan ya nuna jajircewar bangaren shari’armu wajen karfafa damokradiyarmu. Wannan ya cancanci yabawa.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP reshen Kano ta ce ta amince da hukuncin kotun koli da zuciya daya

“Sannan ina kira ga abokan adawarmu na siyasa da su zo mu hada hannu don inganta jihar. Muna da ayyukan cigaba da dama a kasa. Kuma wasu da dama na zuwa,” in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel