Bayan kotun koli, akwai hukuncin Allah – Abba gida-gida

Bayan kotun koli, akwai hukuncin Allah – Abba gida-gida

Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kano na 2019, ya yi martani ga hukuncin kotun koli, wacce ta tabbatar da zaben Abdullahi Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar.

A wani hukunci da Justis Nwali Ngwuta a madadin kwamitin alkalai na mutum bakwai, kotun kolin ta ce karar da Mista Yusuf ya shigar bata da karfi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa a wani jawabi daga kakakin dan takarar gwamnan na Kano, Sanusi Dawakintofa, Mista Yusuf ya yi zargin cewa bangaren shari’a ta yi wasa da damokradiyyar Najeriya wajen yiwa mutanen Kano fashin kuri’unsu.

“Hukuncin yau a kan shari’ar zaben gwamnan Kano ya kara tabbatar da hadewar da aka yi wajen fashin zabe wanda hakan ya kasance zalunci ga damokradiyyar Najeriya.

“Duba ga hujjojin da tawagar kwararrun lauyoyi suka gabatar, mutum zai yi al’ajabin yadda wadannan azzalumai marasa kishin damokraiyya suka hada hannu wajen yiwa al’umman jihar Kano masu karamci fashin kuri’unsu.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP reshen Kano ta ce ta amince da hukuncin kotun koli da zuciya daya

“Sai dai kuma, mun ga iya gudun ruwansu, don haka su jira hukuncin Allah madaukakin sarki, wanda ba za su iya guje masa ba” inji jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel