Yanzu-yanzu: Jigogin APC sun fito zanga-zangar nuna goyon bayan kotu koli a Abuja

Yanzu-yanzu: Jigogin APC sun fito zanga-zangar nuna goyon bayan kotu koli a Abuja

Wasu jigogin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sun fara zanga-zangar nuna goyon baya ga kotun kolin Najeriya, mintuna bayan jigogin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP suka fara zanga-zanga a kotun koli.

Jigogin APC sun taru ne a farfajiyar Unity Fountain sannan suka garzaya sakatariyar tarayya dake kwaryar Abuja karkashin jagorancin Iliya Adama.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara zanga-zangarta da ta shirya a Abuja a safiyar ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, da wasu manyan mambobin jam’iyyar na daga cikin mutanen da ke gagarumin zanga-zangar wanda ke gudana a yanzu haka.

Shugaban jam’iyyar adawa a jawabinsa ya ce ya zama dole kotun koli ta janye hukuncinta kan zaben gwamnan jihar Imo inda ta salami dan takararta, Emeka Ihedioha, sannan ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hope Uzodinma a matsayin sahihin zababben gwamnan jihar.

Ku saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel