Akalla Sojoji 17 sun hallaka, an yi awon gaba da mutane da dama a sabon harin Boko Haram

Akalla Sojoji 17 sun hallaka, an yi awon gaba da mutane da dama a sabon harin Boko Haram

Akalla mutane 17 sun rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da mutane da dama a artabu biyu da akayi ranar Juma'a da Asabar tsakanin Sojoji da Boko Haram a kan titin Bama-Gwoza. The Punch ta ruwaito.

Hakazalika an hallaka yan ta'addan Boko Haram da dama duk da cewa ba'a san adadinsu ba a yanzu.

Yan ta'addan sun kai hari ne kauyen Firgi, hanyar Gwoza zuwa Bama ranar Juma'a.

Bayan sa'ao'i biyu ana artabu tsakaninsu da Sojoji, an yi rashin jaruman Soji 13 yayinda sauran suka yanye.

Majiya daga gidan Soja ya bayyana cewa yan ta'addan sunyi awon gaba da makamai, harsasai da motocin hukumar Sojin Najeriya.

Daya daga cikin majiyoyin yace: "A musayar wutan da akayi misalin karfe 10 na dare, an kashe Sojoji 10 kuma an dauke motocinsu 4.

"A ranar Asabar kuma, yan ta'addan suka dawo wajen domin cigaba daga inda suka tsaya."

A ranar Asabar, yan Boko Haram sun kaiwa Sojoji hari a tashar Banki misalin karfe 10. Sai da aka kwashe sa'o'i uku ana musayar wuta.

Rahoton Punch ya ce Sojoji 4 suka rasa rayukansu amma ba'a san adadin yan ta'addan da aka kashe ba.

Hakazalika ance yan ta'addan sunyi awon gaba da wasu Sojoji tare da sace makamai da harsasai.

Yayinda aka bukaci tsokaci daga bakin kakakin hukumar Soji, Kanar Sagir Musa da Kanal Isa Ado, basuyi martani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel