Yanzu-yanzu: Kotun koli ta dage karar Bauchi da Plateau zuwa karfe 3

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta dage karar Bauchi da Plateau zuwa karfe 3

Kotun kolin Najeriya ta dage zaman sauraron karar zaben gwamnan Bauchi da Plateau zuwa karfe 3 na rana, yau Litinin, 20 ga watan Junairu, 2020.

Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan karar da aka daukaka kan zaben gwamnan jihar Kano.

A madadinsa, Justis Sylvester Ngwuta ke jagorantar kwamitin alkalan mai dauke da mambobi biyar.

Sauran sun hada dan Justis Kudirat Kekekere-Ekun, Justis Olukayode Ariwoola, Justis Amina Augie da kuma Justis Uwani Abba-Aji.

Mun kawo muku cewa kotun koli ta tabbatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, matsayin gwamnan jihar Kano bayan watsi da karar Abba Kabir Yusuf da PDP.

Hakazalika kotun ta yi watsi da karar Ahmad Aliyu Sokoto da jam'iyyar APC inda suka kalubalanci nasarar gwamna Aminu Waziri Tambuwal a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel