Jama’a na tserewa yayinda Boko Haram suka karbe hanyar Damaturu-Maiduguri

Jama’a na tserewa yayinda Boko Haram suka karbe hanyar Damaturu-Maiduguri

Jama’a da dama na tserewa daga gidajensu sakamakon hare-haren yan ta’addan Boko Haram a hanyar babban titin Maiduguri/Damaturu.

Hankula sun tashi a karshen mako sakamakon rashin tsaro a Auno da kewayenta a karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Yan ta’addan na ta addaban masu mota da kauyawan da ke wajen tsawon makonni duk da yawan tashoshin binciken sojoji.

Mazauna yankin sun koka cewa ana kashe mutane da dama sannan ana garkuwa da wasu da dama a kullun.

Wani jigon garin ya ce: “A maraicen nan, sama da mutane 1,000 sun tsere daga gidajensu a Auno, da dama sun koma Maiduguri a ranar Asabar. A yanzu haka da nake magana, manyan motoci na kwashe kayayyakin mutane. Na roke su cewa kada su bari garin ya tarwatse amma sun ki ji.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 5 a Zamfara, sun bayar da lambarsu ta waya

“Ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo mana dauki; mun zabe shi don kawo karshen yakin, amma abun bakin ciki muna komawa baya ta yadda a kullun ake kai hare-hare a hanyar Maiduguri/Damaturu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng