Sarki Sunusi ya so ya gaji Osinbajo lokacin da Buhari ba shi da lafiya – inji Junaidu Mohammed

Sarki Sunusi ya so ya gaji Osinbajo lokacin da Buhari ba shi da lafiya – inji Junaidu Mohammed

Fitaccen muryar adawa a Najeriya, kuma guda daga cikin dattawan yankin Arewacin Najeriya, Malam Junaidu Muhammad ya yi tone tone inda ya fallasa yadda Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya dinga rokon a bashi mukamin mataimakin shugaban kasa a lokacin da shugaba Buhari ke jinya a kasar waje.

Idan za’a tuna a shekarar 2017 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashe sama da kwanaki 100 yana jinya a birnin Landan na kasar Birtaniya bisa wani ciwo da yayi fama da shi, wanda har yanzu ba’a bayyana ma yan Najeriya ciwon ba.

KU KARANTA: Dan majalisar Kano ya dauki nauyin dalibai 100 don karatu a kasar Sudan da Indiya

Sarki Sunusi ya so ya gaji Osinbajo lokacin da Buhari ba shi da lafiya – inji Junaidu Mohammed
Junaidu Mohammed
Asali: Depositphotos

Jaridar The Cables ta ruwaito Junaid ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da yayi da TheInterview inda yace Sunusi ya nemi Osinbajo ya zabe shi mukamin mataimakinsa idan ya dare mukamin shugaban kasa, saboda a tunaninsa shugaba Buhari ba zai kai labari ba.

“A lokacin da Buhari ba shi da lafiya, rashin lafiya yayi tsanani, sai ya tafi wajen Osinbajo, wannan Sarkin Kano mai ci, saboda yana da tabbacin Buhari zai mutu, don haka idan har Buhari ya mutu yana so Osinbajo ya nada shi mataimakinsa, duk da cewa a bayyane ba shi da wata jam’iyya.

“Na sani babu wani mutumi mai hankali da zai yi irin wannan tunanin saboda idan da a ce an sanar da Buhari wannan abin da Sarkin ya yi, kuma idan da Buhari wani shugaba ne na daban da tuni ya yi awon gaba da shi.” Inji shi.

Junaid ya kara da cewa yana sane da lokacin da Sunusi ya tafi wajen Sarkin Legas da Bola Tinubu a lokacin da yake gwamnan CBN yana fada musu cewa akwai dan takarar shugaban kasan da Arewa take so wanda ba Buhari ba, amma Tinubu yace masa ba zasu bi kowa ba sai Buhari saboda shi kadai ne yake kawo kuri’u miliyan 12 a kowanne zabe.

Daga karshe Junaid yace babu wani bukatar kafa wani kwamitin sulhu tsakanin Sarkin Kano da gwamnan jahar Kano, inda yace idan akwai rikici tsakaninsu su biyu su je su sasanta kansu, amma in dai don batun raba masarauta ne bai ga wani abin tayar da kayan bayba, saboda ba’a Kano aka fara ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel