'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 5 a Zamfara, sun bayar da lambarsu ta waya

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 5 a Zamfara, sun bayar da lambarsu ta waya

A ranar Asabar ne wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka kai wani hari tare da yin awon gaba da mutane biyar a kauyen Dogon Daji, Sarkin Noma a yankin karamar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, kamar yadda jarudar Premium Times ta wallafa ranar Lahadi.

Shaidun gani da ido sun sanar da Premium Times cewa 'yan bindigar sun bayar da lambobinsu na waya sannan sun karbi na wasu mazauna kauyen kafin su tafi da mutanen.

'Yan bindigar sun bawa jama'a umarnin su kira su daga baya domin a sasanta a kan adadin kudin fansar da za a kai musu kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa dasu.

Wadanda suka karbi lambobin 'yan bindigar sun bayyana cewa basu samesu ba a ranar Asabar din, sai da safiyar ranar Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammadu Shehu, bai samu damar amsa kiran da Premium Times tayi masa ba ranar Lahadi domin jin ta bakinsa a kan sabbin hare - hare da 'yan bindiga suka dawo kai wa a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 5 a Zamfara, sun bayar da lambarsu ta waya
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 5 a Zamfara
Asali: Twitter

Mazauna kauyen sun bayyana cewa 'yan bindigar su 20 sun zo garin a kan babura tare da yin awon gaba da wasu mutane biyar bayan sun yi wa wasu mutanen kauyen fashi.

Wadanda 'yan bindigar suka yi garkuwa dasu sune; Hakimi Danjuma, Anas Isa, Buba Hakim, Lawalli Olu da wata mace guda daya, Yahanasu Jamilu.

DUBA WANNAN: Gayu da kwalisa: Hotuna 6 na kuruciyar Buhari da suka jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta

Kakakin rundunar atisayen 'ofireshon Hadarin Daji a Zamfara', Ayobami Oni - Orisan, ya ce ba a sanar dasu faruwar lamarin ba.

Amma, ya bayyana cewa zai tuntubi wasu majiyarsu domin neman arin bayani.

Sai dai, Oni bai tuntubi jaridar Premium Times ba har zuwa lokacin data wallafa rahoton faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel